By Fadimafayau


Na san da dama za su yi mamakin taken rubutun nawa na yau, wato cutarwar haƙuri, nima a da na rasa me zan rubuta game da taken sai dai daga baya da na yi wani dan nazari, dukda ba mai yawa ba ne sai na ga dacewar rubutu kan kalmar haƙurin. Sai dai fa wannan haƙurin ba wai na ban haƙurin da muka sani ba ne na an yi maka laifi a nemi afuwarsa, a'a irin cutarwar da kalmar ke ma yawancin mata nake son ɗan yin magana akai.

    Sanin kowa ne tun saka ranar auren yarinya wata ma tun fara soyayyarta za ta fara cin karo da wannan kalmar ta haƙuri.

    Kai da dama ma wasun mu ba wai sai an zo da maganar sun isa aure ba a'a tun yarinta kalmar haƙuri ke fara cutar da su. A yanzu na san kuna ta tunanin ta ya ma za'a yi Haƙuri ko kalmar ki yi Haƙuri zai zama cutarwa. Tabbas ni kam a tawa mahangar ba kadan ba ki yi haƙurin nan ya tsonen ido, ba wai don zamtowa ta cikin masifaffu ba. Sai don lura da cewa mata da dama kalmar ta zamto silar jaza mu su cutar damuwa.

     Sau da dama in muka duba tun daga rayuwar yarinta musamman gidan da basu san me suke ba, idan suna da yara maza da mata, akan fifita mazan kan matan ko da a na yiwa matan komai, saika ga duk rashin kyautawar da yan uwanta maza zasu mata budar bakin mahaifiyar sai dai tace ki yi haƙuri, ke kin cika ƙorafi, saɓanin idan ita ta yiwa wadannan mazan abin rashin kyautawa, haka uwar za tai ta mata fada.
    
     Mace ce duk rashin kyautawar da mijinta zai mata budar bakin kowa shi ne Haƙuri za ki yi. Abin da ke ban mamaki da wannan kamar ta haƙuri, ban cika jin a na faɗawa maza ba, wato in ji a na haƙuri za ka yi, a'a kullin namiji ne me gaskiya, ko da ita takawo ƙara sai an samu mai ɗora mata laifi, musamman a gabansa ƙarshe kuma a sa ta nuna ita ɗin ce me laifin ta nemi afuwa, sai ya bar gurin ka ji a na ai zaman aure ya gaji haka, haƙuri za ki yi. Wani kayan haushi harda yan uwanta mata, abin na ban mamaki har na kan dan tambayi kaina wai su mata haƙurin nan su suka fi kowa, ko mai da komi na rayuwarsu sai a ce haƙuri za su yi? Nan wata za ta fita wani ƙato yaci mata mutunci sai dai a bata haƙuri. Wata ma keta mata haddi za'a yi masu mutunci ne zasu bada haƙuri kawai su yi shiru. Yayin da wasu kafin su nuna haƙuri ya kamata sai sun nuna ita ta jawa kanta, da ba ta yi shiga irin kaza ba, ko ai da ba ki yi kaza ba da ba a yi miki abin da aka yi ba, ƙarshe sai ace tunda ke kika ja ki yi haƙuri abar zancen in abu ya fito ke za ki kwan a ciki.
 
     Bawai ina yin wannan rubutun ba ne don tunzura mata su dai na haƙurin a'a sai don kawai a gyara ba wai ko yaushe ake buƙatar cewar ayi haƙurin ba a'a bayyanar da gaskiya gami da ɗaukan mataki shi ne mafi a'ala. 

Wani abu ko nace babbar illar kalmar nan, shi ne mace za ta kai ƙarar cin zarafi da watakila mijinta ke mata, walau duka zagi ko wani abu akasin haka sai ka ji ana ai shi aure ya gaji haka haƙuri za ki yi, to ni tambaya ta anan shin wai shi auren ina an yi shi ne don kwanciyar hankali da kare mutuncin juna, me ya kawo fadin shi ya gaji haka mai zai hana ko yaya ne in ta kawo ƙarar a duba a dan ɗauki mataki?

Za mu cigaba